Dalilin da yasa bello turji yake neman sulhu
Angano dalilin da yasa bello turji yasako mutanen da yayi garkuwa da su.
ya sako mutane 52 da ya An gano muhimman dalilan da yasa Turji ya sa da yayi garkuwa da su
‘Yan bindiga sun kashe mutum 13, sun yi garkuwa da 46 a Kaduna
Saura kiris sojoji su ga karshen Bello Turji – Tambuwal ya yiwa talakawa albishir
An bayyana wasu manyaan dalilai da ake ganin su suka sanya Bello Turji ya sako mutane 52 da ya yi garkuwa da su a baya
An ruwaito cewa wani zama aka yi na musamman da gwamnati da kuma shugabannin ‘yan bindigar inda hakan ya sanya ya saki mutanen
Kamar yadda rahotanni suka nuna tawagar gwamnati ce ta je har cikinn daji don tattauna da shugaban ‘yan fashin dajin
Wata takarda da ta fito a farkon watan Disambar shekarar 2021 ta ba da rahoton cewa wata tawaga ta kai ziyara yankin da Bello Turji ya ke zama domin samun daman tattaunawa da shi a bisa fatali da ya yi ga me da roko da al’ummar Shinkafin suka yi a baya.
Bello Turji dai shi ne jagoran duk wani kisa da kuma garkuwa da mutane da ke afkuwa a tsakanin kananan hukumomin Shinkafi, Sabon Birni, da Isa a jihohin Zamfara da Sokoto domin neman kudin fansa.
An samu bayanin cewa wadanda aka sako din sun hada da mata, wadanda sune aka fi yawan sace wa, inda hakan ya faru ne bisa biyayya da wasu yaran sarkin ‘yan ta’addan suke yi, yawancin satar mutanen na faruwane a kan hanyar Shinkafi – Isa, Isa – Sabon Birni da Kaura Namoda wanda ke hanyar Shinkafi, a rahoton da Daily Trust ta kawo.
Shugaban ‘yan bindiga Bello Turji
“Wasu daga cikin wadanda aka kaman sun shafe sama da watanni biyu a hannun masu garkuwa da mutanen, wasu kuma an sake su ne bayan da ‘yan uwansu su kayi hakilon biyan kudin fansa.
“Su kuma wadanda iyalansu ba su da karfin da za su iya tara makudan kudaden da aka nema domin fansa da masu garkuwan suka bukata, suna nan a tsare a wurin ya ta’addan har zuwa wannan lokaci da Ubangiji Madaukakin Sarki ya kai musu Agaji,” kamar yanda wani mazaunin garin na Shinkafi ya bayyana wa wakilin Daily Trust haka ta wayar tarho.
“Ba wai kawai a sansanin Bello Turji suke zaune ba, wasu daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su an daukesu zuwa hannun wasu yaran Turji a sansanoni mabanbanta cikin yaran har da wani mai suna Danbokolo. Wani mazaunin yankin ne ya yi kokarin gano wasu daga cikin wadanda aka ajiye a sansanin Danbokolo a lokacin da suke shigewa a motoci”.
Majiyoyi sun bayyana cewa Turji ya fara fuskantar matsananciyar matsin lamba sakamakon hare-haren da sojoji suka kai a yankin wanda ya kai ga hallaka ‘yan uwa da danginsa da dama.
A watan da ya gabata ne Turji ya rubuta wasika zuwa ga majalisar masarautun Shinkafi, inda ya jaddada aniyarsa ta cewa a zo a yi sulhu, tare da kuma daura aniyar ajiye makamai da kuma wanzuwar zaman lafiya. Majiyoyi sun bayyana cewa hakan na daya daga cikin tattaunawa da aka yi da Turji wanda ya kai ga taimakawa wurin sako wadanda aka yi garkuwa da su.
Amma wasu mazauna yankin sun ce Turji na iya shiryawa ya bar yankin gaba daya koda kuwa ba ze ajiye makamansa ba ko kuma ya yi watsi da ta’addanci.
Ya ce duk da kasancewa Turji ya yi kaurin suna saboda ta’asar da ya aikata, babu laifi don anyi zaman tattaunawa da shi amma dai a tabbatar da cewa shi da sauran wadanda suka aikata laifuka sun fuskanci shari’a.
ido ba, sab baya tattaunawa da za a yi ya kamata ace an maslaha.
Comments
Post a Comment