SANATOCIN JAM'IYAR APC SUNA SHIRIN SAUYA SHEKA
Sanatocin APC 22 na shirin sauya sheƙa zuwa jam'iyyun adawa -- Fani-Kayode
Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma ƙusa a jam’iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa wasu Sanatoci 22 na jam’iyyar APC mai mulki kasar nan na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Ya bayyana cewa sunatocin na shirin sauya shekar ne saboda jam’iyyar ta hana su tikitin takara a zaben shekara ta 2023.
Da ya ke bayyana damuwarsa kan ficewar da aka yi a jam’iyyar, Fani -Kayode a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba ya ce dole a yi wani abu don hana kara faruwar hakan.
"Sanatocin APC 22 suna barazanar sauya sheka zuwa PDP saboda an hana su tikitin komawa majalisar dattawa. Wannan yana da mahimmanci kuma dole ne a yi wani abu don hana su.
"Mutane da yawa sun damu sosai kuma mun roki shugaban da sakataren jam’iyyar APC na kasa da su sami sanatoci don hana su, saboda mu baza iya hakurin rasa su ba”. Inji Fani kayode
Da ya ke zantawa da manema labarai bayan ganawar sirri da Sanatocin APC, Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya ce abin takaici ne yadda ‘yan majalisar suka fice daga jam’iyyar.
Sai dai ya ce ana sa ran za su sauya sheka ne saboda dama duk kakar zabe akan sami hakan a Siyasar kasar nan.
A safiyar yau ne jaridar Daily Trust ta rawaito yadda wasu Sanatoci bakwai suka fice daga APC zuwa wasu jam’iyyun adawa.
Mambobin Majalisar Dattawan da su ka fice daga APC sun haɗa da Ibrahim Shekarau (Kano), Yahaya Abdullahi (Kebbi) Adamu Aliero (Kebbi), Dauda Jika (Bauchi), Ahmad Babba Kaita (Katsina), Lawal Yahaya Gumau (Bauchi), da Francis Alimikhena. (Edo).
Comments
Post a Comment