Min menu

Pages

2023: INEC za ta gudanar da zabe da ba a taba mai ingancinsa ba - - yakubu

2023: INEC za ta gudanar da zaɓe da ba a taɓa mai ingancinsa ba -- Yakubu Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, a yau Talata, ta yi alkawarin gudanar da zaɓuka mafi kyawu a Nijeriya a shekarar 2023. Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bada wannan tabbacin a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagogin ' International Republican Institute, IRI, da na National Democratic Institute, NDI, a Abuja. Ya ce taron shi ne na farko da INEC ta shirya bayan zaɓen gwamnan jihar Osun da aka yi ranar Asabar, ya kuma ba da tabbacin cewa za ta inganta nasarorin da ta samu a zaɓukan da ke tafe. “Mun samu kwarin gwiwa da kalamanku masu kyau, amma har yanzu akwai sauran aiki a gaba. “Muna tabbatar muku da cewa ba za mu ƙara dage dantse wajen yin aiki tukuru don ganin mun gudanar da babban zaben 2023 cikin nasara. "Na saurari wasu batutuwan da aka gabatar amma watakila, idan muka shiga zaman aiki za a samu damar mayar da martani ga wasu batutuwa," in ji shi. “Mun yi alkawarin cewa zaɓen Osun zai yi kyau, kuma gashi zaɓen Osun ya yi kyau. Mun yin alƙawarin cewa babban zaɓe na 2023 zai kasance mafi kyawun zaɓen da muka taɓa yi kuma mun himmatu wajen ganin mun samar da mafi kyawun zaɓe a koyaushe, ''in ji shi.

Comments