Min menu

Pages

Gwabnan kano yaba masu rike da mukaman siyasa umurni da suyi murabus

Zaben 2023 : Gwamna Ganduje ya umarci duk masu neman mukaman siyasa da ke rike da muƙami a gwmanatin sa su yi murabus. Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa da ke neman mukaman siyasa a zabe mai zuwa na 2023 da su yi murabus daga mukamansu. Umurnin ya ce "An ba su daga yanzu zuwa Litinin 18 ga Afrilu, 2022, su yi murabus." Domin bin sashe na 84 (12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.

Comments