KABIYA NI 30M KO NA KASHE MUTUM 300.
Nasanda ya ba Matawalle kwana 14 ya biya shi N30m, ko ya halaka rayuka 300
Nasanda, wani shahararren mai garkuwa da mutane a jihar Zamfara ya bai gwamnatin jihar wa'adin kwana 14 da ta biya shi N30 miliyan a matsayin diyyar matarsa da 'yan uwanta biyu.
Ya yi barazanar kashe rayuka 300 idan har ba a cika masa bukatarsa ba, Vanguard ta ruwaito.
Nasanda ya yi ikirarin cewa amaryarsa, kawunta da innarta duk 'yan sa kai ne suka halaka su a jihar.
HumAngle ta ruwaito cewa, a wani sautin murya da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani, Nasanda ya ce da gangan aka kashe masa amaryarsa, kawunta da innarta.
Ya zargi cewa 'yan sa kan sun san cewa suna da alaka da shi.
A sautin muryan, ya ce ya yi matukar adalci kuma bai nuna son kansa ba da ya bukaci N30 miliyan a matsayin diyya.
"Idan da ni mai son kaina ne, zan bukaci N50 miliyan ne a kan kowanne mutum daya," yace.
Kamar yadda yace, "Ba zan bada wa'adin watanni ba, kwanaki 14 na bada kuma a cika bukata ta.
Kuma ba za mu kai farmaki ba sai jama'a suna gonakinsu. Idan ba a kyale Fulani sun yi rayuwarsu cikin kwanciyar hankali ba, mu ma ba za mu bar jama'a su zauna lafiya ba," yace.
"Idan gwamnatin ta kasa biyan kudin, zan yi abinda na saba.
Ina nufin zan halaka rayukan mutum 300 domin daukar fansar mutuwar amaryata da 'yan uwanta biyu.
Tabbas, rayukan mutum 300 za su kasance cikin hatsari," yace a sakon muryar da ya saki.
Menene Ra'ayin ku?
Comments
Post a Comment