Min menu

Pages

Komai girman gona...

Komai girman gona… Tun farkon fitowar shugaba Muhammad Buhari takarar shugaban Kasa abubuwa uku ne Shika-shikan da yake gina yakin Neman zaben sa akansu 1..Farfado da tattalin Arzikin kasa wanda yake zargin PDP ta lalata (dala zata koma daidai da naira) 2..samar da tsaro (what is boko Haram?) 3..Yaki da cin hanci da rashawa ( duk wanda ya saci kudin kasa sai ya dawo dashi” bazan bari a satar muku dukiya ba) Tambaya Dan Allah a ganin ku wanne daga cikin alkawarukan nan Buhari ya cika? Yanzu dai sukuwa ta kare saura zamiya,domin duk abin da Buhari yayi nan da watanni 10 ya zama tsohon shugaban kasa da wane abu zaku tuna dashi,wanne abin mamaki Buhari yayi muku a mulkinsa wanda ya baku mamaki da takaici? Bisimillah

Comments