Min menu

Pages

Yan boko haram sunkai hari a karamar hukumar kujba dake yobe

Menene asalin harufan Hausa? Tambayar da wasu ɗalibai masu koyon sanin makamar aiki suka yi mun a Office dazu. Suna ganin cewa yarukan da suke da asali da tarihi mai tsawo suna da nasu harufan da suke rubutu da su, shin kafin samun harufan turanci da na larabci a tsakanin Hausawa basa rubutu ne, idan suna yi da waɗanne harufan suke rubutawa? Tambayar tasu naga ta dace da abinda zan kawo nan, wa la'alla a samu masana su mana ƙarin haske. A iya sani na akwai ƙabilun Afrika da suke da harufan su na rubutu ba da harufan turanci ko larabci ba, misalin su shine harufan Ge'ez da ake rubuta yaren Amharic da Tigrinya da su, wadanda mutanen ƙasar Habasha da Eritrea suke amfani da shi, tarihi ya nuna cewa harufan na Ge'ez suna da asali tun shekaru 2,000 da suka shuɗe. Akwai harufan Mandombe wadanda aka ce an kirkire su ne a 1970s a Jamhuriyar demokradiyyar Congo dake Afrika ta tsakiya. Suma harufa ne da suke kusan kama da na Ge'ez, ana rubuta yaren ƙabilun Lingala, Kikongo, Swahili da kuma Tshiluba da su. Akwai kuma harufan N'ko da aka kirkira a 1949 wanda ake rubuta yarukan ƙabilun Manding dasu a Afrika ta yamma musamman ma a kasar Mali da kuma Guinea. Harufan suna kusan kama da na larabci, ana fara rubuta su ne daga dama a gangaro zuwa hagu. Yanzu haka ana amfani da harufan wajen koyarwa a Guinea, Ivory coast, da Kuma Mali. (Ina tuna sanda muke yara, mahaifin mu yana rubuta wasiƙa zuwa gambiya da wasu harufa kaman na larabci, amma kuma Yaren Mandinko ne da salon rubutu irin na N'ko) Sai kuma Harufan Vai, Wanda aka kirkire su a 1830. Da harufan ake rubuta yaren Vai na mutanen Laberiya, suna amfani da harufan lambobi na larabci, amma kuma harufan sa sunfi kama da na Mandarin, alamomi ake zana wa na wasu abubuwa da suke bada ma'anar wata kalma ko jumla. Da ma waɗansu da dama. Shin yaren Hausa ko Filatanci na da nasu harufan da ake rubuta su a asali kafin tasirin harufan turawa da na larabawa? Daga Aliyu samba.

Comments