Buhari ya gana da Gwabnonin APC
Buhari na ganawar sirri da gwamnonin APC kan wanda zai yi wa Tinubu mataimaki
Shugaban Ƙasa asa Muhammadu Buhari na ganawar sirri da wasu gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa da ke Abuja.
Gwamnonin sun samu jagorancin Shugaban kungiyar Gwamnonin APC, PGF, Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi.
Waɗanda suka halarci ganawar sun haɗa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; Sakataren gwamnatin tarayya, SGF, Boss Mustapha; Gwamna Babagana Zulum na Borno da Nasir El-Rufai na Kaduna.
Sauran sun haɗa da Gwamna Mohammed Badaru Abubakar na Jigawa; Abdullahi Sule na Nasarawa; Simon Lalong na Filato; Yahaya Bello na Kogi da Hope Uzodinma na jihar Imo.
Duk da dai ba a bayyanawa manema labarai maƙasudin taron ba, DAILY NIGERIAN ta tattaro cewa ganawar ba za ta rasa nasaba da yunƙurin zaɓar wanda zai yi wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ba mataimaki.
Idan ba a manta ba, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana cewa ranar 17 ga watan Yuni ne wa’adin mika sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakan su zai ƙare.
Comments
Post a Comment