Min menu

Pages

Yan Bindiga sun saki mutanen da suka kama a harin jirgin kasan kaduna zuwa Abuja.

'Yan Ta'adda Sun Saki Wasu Daga Fasinjojin Jirgin Kasan Abuja-Kaduna Da Suka Sace Aliyu Samba Wasu ‘yan ta’adda da suka kai hari kan wani jirgin kasa da ke kan hanyar Kaduna a ranar 28 ga Maris, 2022, sun sako wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su. ‘Yan ta’addan sun kai harin bam a wani sashe na titin jirgin, lamarin da ya tilasta wa jirgin tsayawa, kuma yan ta'addan suka budewa fasinjojin wuta, suka kashe mutane tara tare da yin awon gaba da 62 da suka hada da yara da tsofaffi. Daily Trust ta ruwaito cewa bayan shafe kusan kwanaki 74 a hannun yan ta'addan, an sako mata shida da maza biyar a ranar Asabar bayan wata tattaunawa da yan ta'addan. Mawallafin Jaridar Desert Herald, Tukur Mamu, wanda ya kasance mai shiga tsakani yayin tattaunawar ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce majiyar sa ta shaida masa cewa ‘yan ta’addan sun sako mazan cikin su ne bisa la’akari da lafiyarsu, inda ya ce matan kuma sanoda kasancewar su daga cikin masu rauni.

Comments