Da-Dumi Dumi: Jam'iyar Apc Ta Ayyana Tinubu A matsayin baya cikin hayyacin sa
Jam'iyyar APC ta mayar wa tsohon gwamnan Legas Ahmed Bola Tinubu da martani kan kalaman da ya furta game da Buhari da suka tada ƙura a Najeriya.
Shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya ce ba su ji dadin kalaman ba musamman daga Tinubu da ake kira jagoran jam’iyyar.
"Bai kamata ya kawo zancen abin da bai shafi Buhari ba, har ya ambaci sunansa ba, wanda mutum ne da muke ganin kimarsa a rayuwar jam’iyyarmu," in ji shi.
Ya ce kuskure ne ya ambaci Buhari a wurin da ba ya nan.
Daga baya Tinubu ya fito ya ce ba a fahimci kalamansa ba ne, yana mai cewa yana matukar mutunta shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kuma ba zai taba raina shi ba.
Amma Shugaban APC Abdullahi Adamu ya bayyana kalaman na Tinubu a matsayin “kururuwa bayan yaƙi” yana mai cewa kamata ya yi ya je ya ba Buhari hakuri.
“Ni ina ganin Tinubu ba ya cikin hayyacinsa lokacin da ya yi kalaman,” in ji Abdullahi Adamu.
Shugaban na APC kuma ya ce dukkanin masu neman shugaban ƙasa mutum 23 za su yi takara a zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar za ta gudanar, sabanin rahotannin da ke cewa an cire
Comments
Post a Comment