Min menu

Pages

Gwabnonin Arewa Sun Aminta Mulki Ya Koma Kudu:

Gwamnonin Arewa na jam'iyyar APC sun goyi bayan mulki ya koma Kudancin Kasar, inda suka ce ya dace wani yanki ya karbi ragamar mulki bayan Shugaba Muhammadu Buhari na tsawon shekaru takwas. A wata sanarwa da suka fitar a ranar Asabar, akalla gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 11, sun ce a takaita nemo wanda zai gaji Buhari a Kudu. “Gwamnonin jam’iyyar APC da shugabannin siyasa daga jihohin arewacin Najeriya a yau sun yi taro domin duba yanayin siyasa da kuma kara marawa jam’iyyar mu baya wajen samar da shugabanci na gari a cikin kalubalen da muke fuskanta a kasa. A tattaunawar tamu, mun yi maraba da gayyatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wa gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki magana domin su ba da gudummuwarsu wajen ganin an samu dan takarar shugaban kasa mai karfi a jam’iyyar APC.” “Bayan mun yi taka-tsan-tsan, muna so mu bayyana tabbacinmu cewa bayan shekaru takwas na mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 ya zama daya daga cikin jiga-jigan ‘ya’yanmu daga jihohin kudancin Najeriya. Mun tabbatar da cewa kiyaye wannan ka'ida yana da muradin gina kasa mai karfi, hadin kai da kuma samun ci gaba". “Saboda haka muna so mu ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara mai karfi cewa neman wanda zai gaje shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya takaita ga ‘yan uwanmu daga jihohin Kudu. Muna kira ga duk masu son tsayawa takara daga jihohin Arewa da su janye don amfanin kasa, su bar masu neman kudu kawai su ci gaba da zaben fidda gwani. Mun ji dadi da shawarar da abokin aikinmu mai girma Gwamna Abubakar Badaru ya dauka na bayar da gudumawa a wannan fafutuka ta kishin kasa ta hanyar janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa". "Jam'iyyar APC tana da alhakin tabbatar da cewa zaben 2023 ya ba da damar gina kasa, tare da tabbatar da cewa tsarin dimokuradiyya ta kasance ga duk wanda ya amince da hadin gwiwa da gina tsarin kasa. A wannan karon yana bukatar a bi tsarin da ya dace wajen zabar dan takarar jam’iyyarmu, kuma muna kira ga dukkan shugabannin jam’iyyar APC da su sauke nauyin da ke kansu a kan hakan.”

Comments