Buhari Ya Roki Yan Nigeria Da kada su Bari PDP Ta Mulke su.
Buhari ya roƙi 'yan Najeriya 'kada ku ƙyale PDP ta mayar da Nijeriya baya'
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga 'yan Najeriya su tabbata ba su bar jam'iyyar adawa ta PDP "ta mayar da ƙasa baya ba".
BBC Hausa ta rawaito cewa da yake jawabi a wurin zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyarsu ta APC, Buhari ya ce APC ta sauya Najeriya ta hanyar gudanar da ayyukan raya ƙasa.
"Wajibi ne mu zaɓi masu adalci 'yan kishin ƙasa da ke da aƙidar haɗa kan ƙasarmu...don ciyar da ita gaba.
"Bai kamata mu ƙyale PDP ta mayar da Najeriya baya ba."
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoton PDP ba ta mayar da martani ba, wadda tuni ta zaɓi Atiku Abubakar a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a babban zaɓe na 2023.
Comments
Post a Comment