Min menu

Pages

Yau makiyan Talakawa bazu iya bacci da na zama Dan Takarar shugaban Kasa kwankwaso.

'Yau maƙiyan talakawa ba za su iya bacci da na zama ɗan takarar shugaban ƙasa ba' -- Kwankwaso A yau Laraba ne tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zama ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP a zaɓen fidda-gwani na shugaban kasa na jam’iyyar. Dalaget 774 na jam’iyyar daga jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja ne suka zaɓe shi baki ɗaya ta hanyar kaɗa ƙuri’a. Da ya ke jawabi bayan an sanar da shi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Kwankwaso ya bayyana cewa a yau rana ce ta farin-ciki sabo da sunansa zai fito a kan ƙuri'ar zaɓe a karon farko. A cewar Kwankwaso, samun tikitin takarar shugaban ƙasa zai zame wa wasu wanda ya siffanta da "maƙiyan talakawa" barazana, inda ya ce "yau maƙiya talakawa ba za su iya bacci ba da na zama ɗan takara. Su na ta yi mini bita-da-ƙulli domin su daƙile ni". Tsohon Sanatan ya ƙara da cewa jam'iyar NNPP jam'iya ce da kudirin ta shine "samar da haɗin kai, zaman lafiya, daidaito, bunƙasar arziki da ilimi. "Ina kira ga ƴan ƙasa da ku je ku yanki katin zaɓe domin ƙarshen watan nan na Yuni za a rufe. Ƙuri'ar ku ita ce jarin ku. Ina kira gare ku da ku je ku yanki katin zaɓe ku kuma zaɓi NNPP. "Daga alamar kayan marmari na jam'iyar mu an san cewa jam'iya ce ta ceton talakawa," in ji Kwankwaso.

Comments